✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda sojoji da ’yan siyasa suka kassara kananan hukumomi —Obasanjo

Ya ce halin da Kananan Hukumomi suke ciki a halin yanzu sai addu'a

Tsohon Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo ya dora laifin tabarbarewan al’amura a Kananna Hukumomin kan gwamnatocin soji da ’yan siyasa da suka shugabanci Najeriya.

Obasanjo ya sha’anin kananan hukumomi ya fara tabarbarewa ne tun lokacin da shugabannin soji suka so samun kananan hukumomi a jihohinsu, daga baya kuma ’yan siyasa suka kara lalata al’amura ta hanyar almundahana.

Sanarwar da kakakinsa, Kehinde Akinyemi, ya fitar ranar Talata ta ruwaito shi yana cewa tabarbarewar ta kai yadda kanan hukumomi 774 da ke kasar ba su da ko gireda da za a iya gyara hanya da ita, kamar yadda Dokar Kananan Hukumomi ta 1979 ta tana.

Yayin ganawarsa da Shugaban Kungiyar Ma’aikatan Kananan Hukumomin Najeriya na Kasa (NULGE), Kwamared Akeem Olatunji Ambali, wanda ya ziyarce shi a gidansa da ke Abeokuta, Tsohon Shugaban Kan ya bayyana cewa a halin yanzu, dorewar kananan hukumo na Najeriya “yana hannun Allah,” duba da yadda gwamnoni suka yi watsi da gyare-gyaren da dokar Kananan Hukumomin ta tanada.

Don haka ya yi kira ga ma’aikatan kananan hukumomi su ci gaba da addu’o’i domin ganin abubuwa sun inganta.

Tun da farko Shugaban NULGE na kasa ya shaida wa Obasanjo cewa kungiyar na bukatar dauki game da yunkurin Majalisar Tarayya na soke Kananan Hukumomi da Kundin Tsarin Mulkin 1999.

Ambali ya bayyana kudurin dokar a matsayin yunkurin kashe shugabancin kananan hukumomi a kasar.