✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda yajin aiki ya tsayar da harkoki a Kaduna

Tun da safiya masu yajin aikin suka rufe ma'aikatun Gwamnatin Jihar Kaduna.

Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) na gangami bayan ta fara yajin aiki saboda korar ma’aikata da wasu tsare-tsaren Gwamnatin Jihar Kaduna da ta ce kuntatawa ne ga ma’aiakta.

NLC ta fara yajin aikin ne bayan Gwamnatin Jihar ta ce babu gudu, babu ja da baya a sallamar da ta yi wa dubban ma’aikatanta a baya-bayan nan.

Tun da sanyin safiyar Litinin NLC ta rufe tashar jirgin kasa da ke Rigasa, da Asibitin Koyarwa na Barau Dikko da Sakatariyar Gwamnatin Jihar, wadda a cikinta 10 daga cikin Ma’aikatu n Gwamantin Jihar suke.

Kafin su fara tattaki a kan tituna bisa jagorancin Shugaban NLC na Kasa Ayuba Wabba, jami’an kungiyar sun bi ofisoshin Gwamnatin Jihar suna kullewa da zimmar tabbatar da tsayawar harkoki ci a ma’aikatun.

Ga wasu hotunan yajin aikin:

Shugaba NLC na kasa Ayuba Wabba ne ya jagoranci tattakin masu yajin aikin bayan ya yi ‘yan kwadago jawabi a Kaduna.
Wasu daga cikin ‘yan NLC a lokacin da suke tattakin a ranar Litinin da safe a garin Kaduna.
Tashar jirgin kasa da ke Rigasa ta kasance a rufe saboda yajin aikin kungiyar kwadagon.
Likitoci da ma’aikatan jinya sun shiga yajin aikin inda aka aka rufe Asibitin Koyarwa na Barau Dikko.
Marasa lafiya sun rika komawa gidajensu daga Asibitin Koyarwa na Barau Dikko bayan ma’aikatan lafiya sun shiga yajin aikin.
Shigar jami’an kiwon lafiya cikin yajin aikin ya jefa marasa lafiya a Asibitin Koyarwa na Barau Dikko cikin halin ni ‘yasu.
Da sanyin safiyar Litinin jami’an NLC suka kulle kofar Sakatariyar Gwamnatin Jihar Kaduna.
Layin motocin ma’aikata a kofar Sakatariyar Gwamnatin Jihar Kaduna, a yayin da NLC ke tabbatar da yajin aikin.