✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yajin aikin Kaduna: Al’amura sun yi tsaya cik a Zariya

Al’amura sun tsaya cik a garin Zariya sakamakon yajin aikin da Kungiyar Kwadago ta Kasa, NLC, ke yi a fadin Jihar Kaduna. Wakilin Aminiya wanda…

Al’amura sun tsaya cik a garin Zariya sakamakon yajin aikin da Kungiyar Kwadago ta Kasa, NLC, ke yi a fadin Jihar Kaduna.

Wakilin Aminiya wanda ya zaga garin ya shaida yadda bankuna da Sakatariyar Karamar Hukumar Zariya da Asibitoci da gidajen mai har ma da makarantun firamare da na sakandare suka kasance a garkame.

Wakilin namu ya ce a Asibitin Gambo Sawaba da ke Kofar Gayan wasu marasa lafiya na ta komawa gida saboda rashin masu kula da su.

Wasu daga cikin Asibitocin Gwamnatin Kaduna da suka kasance a kulle

 

Wasu marasa lafiyar sun yi kira ga Kungiyoyin Kwadagon da Gwamnatin Jihar Kadunan da su sami maslaha domin talaka ya sami saukin rayuwa.

Kungiyar ta tsunduma yajin aikin da ta kira na gargadi na kwana biyar a safiyar Litinin kan matakin da Gwamnan Jihar, Malam Nasir El Rufai ya dauka na sallamar ma’aikata sama da dubu biyu daga bakin aiki.

Sakatariyar Karamar Hukumar Zariya a kulle yayin yajin aikin da ma’aikata ke yi.