✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kashe mai gari a Sakkwato

'Yan bindiga sun shiga kauyen Tunga, inda suka kashe mai gari tare da wasu biyu.

Wasu ’yan bindiga sun harbe mai garin Tunga har lahira tare da wasu mutum biyu a Karamar Hukumar Illela, a Jihar Sakkwato.

Aminiya ta gano ’yan bindigar sun kai farmakin ne gabannin Sallar Magriba, a ranar Laraba.

Wani mazaunin garin, ya shaida wa wakilinmu cewa ’yan bindigar suka dauki tsawon awa guda suna cin karensu babu babbaka kafin su fice daga garin.

Aminiya ga gano cewa ’yan bindigar sun kai hari kauyen Nasarawa da ke Karamar Hukumar Sabon Birni a ranar Larabar, sai dai babu wanda ya rasa ransa.

Ibrahim Adamu, ya bayyana cewa maharan sun kai harin a kafa ne, da misalin karfe 10:30 na safe.

“Sun shiga gidajenmu tare da karbe kudadenmu da kayan amfani.

“Sun zane matan da mazajensu suka gudu a yayin harin,” a cewar Adamu.

Ya kara da cewa babu wanda suka kashe ko suka yi garkuwa da shi, sai dai sun yi awon gaba da dabobbi da yawa na jama’ar kauyen.

Kakakin ’yan sanda a Jihar Sakkwato, ASP Sanusi Abubakar ya tabbatar da faruwar harin biyu.

Sai dai ya ce rundunar Kan Kace Kwabo (Operation Puff Adder), ta shiga yankunan don fatattakar maharan.