✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

`Yan bindiga sun kona sama da gidaje 25 a Chibok

Wasu da ake zargin ‘yan Boko Haram ne, sun kona wani kauye a Karamar hukumar Chibok ta jihar Borno jiya Laraba kamar yadda ‘yan bangan…

Wasu da ake zargin ‘yan Boko Haram ne, sun kona wani kauye a Karamar hukumar Chibok ta jihar Borno jiya Laraba kamar yadda ‘yan bangan garin suka sanar.

An kai harin ne a kauyen Mbolakel kusa da garin Chibok da misalign karfe 1:00 na tsakar dare.

Majiyarmu ta gano cewa, ‘yan bindigan sun bude wa jama’ar garin wuta ne lokacin da suka shiga garin tare da raunata jama’a da dama da kuma kone gidaje yayin da kuma suka kwashe abincin mazauna garin.

An dai kona sama da gidaje 25 a kauyen.