✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan gudun hijira 800,000 ne a sansanoni ke bukatar tallafin abinci – Zulum

Kakakin gwamnan, Isa Gusau ne ya sanar da hakan ranar Juma’a a Maiduguri.

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya roki tallafin gagawa daga Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) kan halin da ’yan gudun hijira sama da 800,000 suke ciki a sansanoninsu a yankunan da ayyukan ta’addanci ya daidaita a jihar.

Kakakin gwamnan, Isa Gusau ne ya sanar da hakan ranar Juma’a a Maiduguri.

Isa ya ce gwamnan ya yi rokon ne a wata wasika da ya aike wa da hukumar lokacin da ya ziyarci shalkwatarta a Abuja ranar Alhamis, inda ya ce ’yan gudun hijirar dake garuruwa 11 na cikin mawuyacin hali.

Garuruwan da gwamnan ya shaida wa hukumar na bukatar tallafin sun hada da Monguno, Bama, Damboa, Gwoza, Dikwa, Gamboru, Ngala, Damasak, Banki, Pulka da kuma Gajiram.

Kakakin ya kuma ce gwamnan ya yaba wa tallafin da NEMA, Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Gabas (NEDC) da kuma Hukumar Hana Fasakwauri ta Kasa, biyo bayan umarnin shugaban kasa na raba kayan abincin da suka kwace a cikin shekaru biyu ga yankunan da ake fama da rikici.

Sanarwar ta kuma Ambato Babban Daraktan hukumar ta NEMA na kara tabbatarwa da gwamnan cewa hukumarsa za ta ci gaba da tallafawa jihar, yana mai yaba wa namijin kokarin da gwamna Zulum ke yi na bunkasa jihar, duk kuwa da kalubalen tsaron da take fuskanta.

Shugaban ya kuma yi alkawarin ci gaba da ba da goyon bayan hukumar musamman wajen ganin kudurin tsarin ciyar da jihar gaba na shekaru 25 masu zuwa da gwamnan ya kirkiro ya zama gaskiya.