✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun cafke masu satar mutane a Filato

An ceto mutum biyu daga cikin wadanda ’yan bindigar suka yi garkuwa da su.

Rundunar ’Yan Sandan jihar Filato ta cafke wasu masu garkuwa mutane hudu, ta kuma kubutar da mutum biyu daga hannunsu.

Kakakin Rundunar, Gabriel Ubah, ya ce rundunar na ci gaba da kokarin ceto ragowar mutum biyu da suka rage ba a gansu ba.

Ya kara da cewa ’yan bindigar sun kai hari ne a yankin Gaya da ke kusa da Chichim a Karamar Hukumar Mangu, da misalin karfe 8:30 na dare.

Sai dai ’yan sanda da ’yan banga sun bi sawunsu, suka kama hudu daga cikinsu tare sa tseratar da mutum biyu.

Bayan cafke ’yan bindigar, an samu manyan bindigogi biyu da harsasai da yawa a tare da su.

Shugaban Karamar Hukumar Mangu, Lawrence Danat, ya yi Allah wadai da ayyukan ’ynn bindigar, inda ya roki jami’an tsaro da su kubutar da ragowar mutanen da ke hannunsu.

Ya kuma jinjina wa jami’an tsaro kan yadda suka bi sahu tare da cafke ’yan bindigar.