✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Yan sanda sun kashe ‘yan bindiga biyu a Zamfara 

'Yan sanda sun yi artabu da su kafin daga bisani suka yi nasarar kashe su.

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Zamfara ta kashe wasu ‘yan bindiga biyu a hanyar Anka zuwa Gummi yayin da suke yunkurin safarar makamai.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Muhammad Shehu wanda ya bayyana hakan a ranar Lahadi, ya ce ‘yan bindigar na jigilar manyan makamai da alburusai daga Taraba.

Ya bayyana cewa an datse ’yan bindigar ne dauke da makamai a cikin wata motar kirar Toyota Corolla.

Bayanai sun ce motar dai na dauke da kunshin harsasan bindiga guda uku, da bama-bamai guda uku, harsasai na bindiga AK 47 har guda 151, harsasai guda 200 na bindigogin kakkabo jiragen sama da kuma layu iri-iri.

“A ranar 7 ga watan Janairu, jami’an ‘yan sanda sun yi nasarar kashe wasu ‘yan bindiga biyu a kan hanyar Gummi zuwa Anka a wani artabu da suka yi na tsawon sa’o’i.

“Nasarar ta samu ne biyo bayan bayanan sirri da aka samu game da zirga-zirgar wadanda ake zargin a cikin wata mota kirar Toyota Corolla dauke da makamai daga sansanin ‘yan ta’addan Taraba da ke kan hanyar Zamfara.

“Biyu daga cikin wadanda ake zargin sun samu munanan raunuka yayin da wasu kuma suka tsere.

“An kai wadanda ake zargin zuwa Asibitin Kwararru na Yariman Bakura da ke birnin Gusau, sai dai daga bisani likita ya tabbatar da mutuwarsu.

“Binciken da jami’an suka gudanar ya kai ga kwato makamai da alburusai.

“Bugu da kari, an tura jami’an ‘yan sanda na sauran jami’an tsaron hadin gwiwa ciki har da ‘yan banga zuwa wurin domin gudanar da bincike da zummar cafke wadanda suka gudu,” in ji Shehu.

Ya ce Kwamishinan ‘Yan sandan jihar, Kolo Yusuf, ya ba da tabbacin aniyar ‘yan sandan na kawar da ‘yan ta’adda da sauran masu miyagun ayyuka a fadin jihar.