✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan sanda sun yi ajalin wani mutum a Kano

Sun harbe shi ne a wuyansa a lokacin da yake zaune a bayan gidansa

’Yan sanda sun harbe wani mutum mai suna Muntari Bala har lahira a unguwar Kwalli da ke Karamar Hukumar Birni a Jihar Kano.

A cewar dan uwan marigayin, Yakubu Babangida wanda ma’aikaci ne a Hukumar Kula da Zirga-Zirgar Ababen Hawa ta Kano (KAROTA), ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 9:30 na daren ranar Juma’a.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, wadanda ake zargin – Holanda da Gaddafi – dukkansu jami’ai ne ofishin ‘yan sandan Kwalli da ke daura da Masarautar Kano a birnin na Dabo.

An ruwaito cewa jami’an sun harbi Muntari a wuyansa, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwarsa.

Duk da dai babu wasu cikakkun bayanai, an samu cewa dai takaddama ce ta rincabe tsakanin mamacin da jami’an biyu tun a ranar Alhamis, kuma ana zargin Holanda ne ya yi harbin da ya yi ajalin matashin.

Babangida ya yi bayanin cewa, “Sun harbe shi ne a wuyansa a lokacin da yake zaune a bayan gidansa jim kadan bayan ya dawo daga wani kauye da ya je sayen abincin dabbobin da yake kiwo.

“’Yan sandan da dan uwana duk an san su a unguwar kuma akwai mutane a lokacin da Holanda ya yi ikirarin kashe shi, kuma kwatsam sai ga shi jiya sun zo sun harbe shi.

“Mun yi kokarin jin bahasin lamarin daga bakin jami’in ‘yan sanda amma duk ofishin ‘yan sandan da muka je sai a yi watsi da mu.

“Sai dai kawai a ce mana mu kai shi asibiti a cire harsashin da ke wuyansa ba tare da an hada mu da ko jami’i daya ba.

“Sai da suka ga mun nace ne sannan aka hada mu da wani dan sanda daya wanda ya yi rakiyar mu zuwa Asibitin Kwararru na Murtala Mohammad.

Aminiya ta yi kokarin jin ta bakin mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, sai dai har ya zuwa lokacin hada wannan rahoto wayarsa tana kashe.