✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan wasan Laliga 138 sun kamu da COVID-19

’Yan wasan gasar Laliga 138 ne hukumomi suka tabbatar da harbuwarsu da cutar COVID-19.

Hukumar Kwallon Kafa ta Kasar Spain ta tabbatar da kamuwar ’yan wasa 138 da cutar COVID-19 a gasar Laliga, yayin da ake kokarin ci gaba da gasar a ranar Juma’a 31 ga watan Disamba.

Rahoton na zuwa ne bayan gwamnatin kasar Spain ta fitar da sanarwar ba wa ’yan kallo kashi 75 cikin 100 damar shiga filayen wasanni don yin kallo.

Duk da haka ana sa ran za a ci gaba da gudanar da gasar ta Laliga, ba kamar gasar Firimiyar Ingila ba, wadda aka dage wasu wasanni sakamakon harbuwa da cutar da wasu ’yan wasa suka yi.

Barcelona na daga cikin kungiyoyin da COVID-19 ta fi yi wa cikas, inda ’yan wasanta 10 suka harbu, daga cikinsu har da Coutinho, Dani Alves, Gavi da Jordi Alba, dukkansu kuma ba za su buga wasan da kungiyar za ta yi da Mallorca ba.

Real Madrid na da ’yan wasa hudu da suka kamu da cutar, bayan mutum 11 da suka warke a baya-bayan nan — Vinicius Jr, Thibaut Courtous, Fede Valverde da Eduardo Camavinga na daga cikin wadanda suka harbu.

Ita ma Atletico Madrid na daga cikin manyan kungiyoyin Laliga da ke fama da COVID-19, inda wasu daga cikin ’yan wasanta da kocinta Diego Simeone da suka kamu da cutar ba za su halarci wasanta a karshen mako ba.

Kungiyar Elche na da mutum 12 da suka kamu, amma duk da haka kungiyar na sa ran buga wasanta a karshen mako, kamar yadda jaridar MARCA ta rawaito.