✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Za a fara amfani da kati na musamman yayin aikin Hajji

Saudiyya ta ce za a fara amfani da katin na musamman a aikin Hajjin 2021.

Ma’aikatar Aikin Hajji da Umrah ta Kasar Saudiyya, ta kaddamar da sabuwar manhaja mai amfani da katin shaida da zai taimaka wa dukkan ayyukanta musamman wajen lura da masu kai ziyarar sauke farali da Umrah.

Za a bai wa mahajjata da masu Umrah katin, wanda zai kasance dauke da duk wasu bayanansu da suka danganci na lafiya da kuma masaukinsu yayin da suke kasa mai tsarki.

Katin zai taimaka wa masu gudanar da aikin Hajji da Umarah wajen gane masaukinsu, sannan za a ribaci katin wajen rage aikata migayun laifuka.

An kaddamar da wannan sabuwar kirkira ce wadda ta yi daidai da kiran da Cibiyar Al’adu ta Makkah da ta yi.

Kirkirar katin mai kunshe da bayanan masu ziyarar sauke farali wani sabon tsari ne wanda yake kan tafarkin yi wa ci gaban fasahar sadarwar ta zamani hangen nesan wanda zai taimaka wajen yi wa mahajjatan hidima.

Za a fara amfani da wanann sabon katin a aikin Hajjin 2021, a matsayin gwaji, inda za a raba kati dubu 50 ga mahajjata.

Za a rika bincikar tasirin tsarin gudanarwar da katin ta hanyar amfani da wata gamammiyar hanya ta fasahar sadarwa.