✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a yi wa yara miliyan 1.7 rigakafin shan-inna a Jigawa

Jihar ta daura damarar kawo karshen cutar shan inna.

Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko ta Jihar Jigawa (PHCDA), ta ce za ta yi wa yara miliyan 1.7 rigakafin allurar cutar shan inna karo na biyu a jihar.

Dokta Kabir Ibrahim, Sakataren Zartarwa na hukumar ya shaida hakan yayin ganawarsa da Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN) ranar Lahadi a Dutse, babban birnin Jihar.

  1. Yadda gayyatar da Majalisa ta yi wa Alkalin Alkalan Kano ta tada kura
  2. Taliban ta kai hari filin jirgin saman Kandahar a Afghanistan

A cewarsa, an tanadi isassun ma’aikata don saukaka gudanar da wannan aiki a duk fadin jihar.

Ibrahim ya ce hakan zai tabbatar da cewa an yiwa dukkan yara ’yan kasa da shekaru biyar rigakafin cutar.

Ya ce hukumar ta samu isassun alluran rigakafin cutar shan inna (OPVs), lamarin da ya ce zai taimaka wajen samun nasarar gudanar da da aikin ba tare da wani kalubale ba.

Sakataren wanda ya nemi goyon baya da hadin kan shugabannin al’umma da na addini da sauran masu ruwa da tsaki, don gudanar da aikin cikin kwanciyar hankali, ya bukaci iyaye da su kai ’ya’yansu zuwa cibiyoyin da aka tanada.

“Iyaye su hada kai da jami’an rigakafi don gudanar da aikin ba tare da an samu wata matsala ba.

“Kuma daga binciken da na yi a wasu yankuna da kuma rahotannin da hukumar da hukumar ta samu, wannan aiki yana gudana cikin kwanciyar hankali a fadin jihar,” in ji Ibrahim.

A cewarsa, irin wannan hadin kan zai taimaka wajen gaggauta daukar matakan yaki da cutar tare da magance sauran matsaloli a jihar.

NAN ta ba da rahoton cewa aikin wanda za a gudanar da shi cikin kwanaki biyar da aka fara a ranar 31 ga Yuli, yana gudana lokaci guda a duk Kananan Hukumomi 27 na jihar.