✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben 2023: Yadda Kwankwaso ya shiga rintsi

Zabi uku da suka rage wa Kwankwaso game da takararsa a babban zaben 2023

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya shiga rintsi a yayin da dambarwar zaben 2023 ke kara kankama.

Majiyoyi masu tushe daga bangaren Kwankwaso sun tabbatar wa Aminiya cewa nan ba da jimawa ba zai sanar da alkiblarsa game da zaben 2023.

Aminiya ta gano cewa babu tabbacin Kwankwaso zai yi takarar shugaban kasa a Jam’iyyarsa ta PDP a 2023, duba da rikicin cikin gidan jam’iyyar a kan karba-karbar mulki, wanda yankin Kudu ke so su samu a wannan karon.

Duk da haka, a matsayinsa na gogaggen dan siyasa ya, Kwankwaso na nazarin abin da ke kasa da kuma irin damar da yake da ita a zaben da ke tafe.

A halin yanzu, lissafin abubuwa uku tsohon gwamnan, wanda ya nemi takarar shugaban kasa a 2015 da 2019, ya fi ba wa karfi.

Masana siyasar Kano, cibiyar tafiyar Kwankwasiyya, na ganin shirun jagoran na Kwankwasiyya alama ce cewa akwai abin da yake shiryawa a karkashin kasa.

Wannan kuwa ya kunshi yiwuwar sauya sheka daga PDP, ko kuma kafa wata sabuwar, ko kuma ya tsaya a PDP, wadda ya koma cikinta a kakar zaben 2019.

Kafa sabuwar tafiya

Wani jigo a tafiyar Kwankwasiyya ya ce jagoransu na buda abubuwa uku, wanda na farko shi ne kafa wata sabuwar tafiya.

“Na san daga farkon wannan wata (Fabrairu) zuwa farkon watan Maris, shi da manyan ’yan siyasa da ya hada za su bullo da wata sabuwar tafiya – ba jam’iyya ba,” inji shi.

Ya ce duk wasu makusantan Kwankwaso irin su Buba Galadima da Sanata Suleiman Hunkuyi na son tafiyar ta rikide zuwa jam’iyyar siyasa, amma Kwankwaso bai goyi bayan hakan ba.

“Yana ganin kafa sabuwar jam’iyya ba zai yiwu ba domin da wuya jam’iyyar ta samu rajista kafin 2023, shi ya sa yake son a yi amfani da sabuwar tafiyar domin cim-ma yarjejeniya da wata jam’iyya,” inji majiyar.

Osinbajo na zawarcin Kwankwaso

Aminiya ta gano cewa bangaren Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo, daga Jam’iyyar APC mai mulki na zawarcin Kwankwaso.

Har yanzu dai Osinbajo bai bayyana matsayinsa game da tsayawa takarar shugaban kasa a 2023 ba.

Wata majiya mai tushe a bangaren Kwankwaso ta shaida wa Aminiya cewa Osinbajo da Shugaban Riko na APC, Mai Mala Buni suna zawarcin Kwankwaso ya dawo jam’iyyar.

“Akwai kwakkawarn tattaunawa tsakanin oga da su, suna so ya dawo APC amma yana nazari, ba ya cim-ma matsaya ba har yanzu,” inji majiyar tamu.

Da aka tambaye shi ko mai gidansa zai karbi tayin kujerar mataimakin shugaban kasa da Osinbajo a matsayin shugaban kasa, sai ya ce, kofar Kwankwaso a bude take.

Ya kara da cewa, “Ba a kai ga yanke shawara ba, amma ina tabbatar muku cewa ana ci gaba da tattaunawa.”

Mun yi kokarin jin ta bakin Mashawarcin Mataimakin Shugaban Kasa kan Harkokin Siyasa, Babafemi Ojudu, a kan lamarin, amma hakarmu ba ta cim-ma ruwa ba.

Idan ba a manta ba, a watan Janairu, Ojudu, wanda magoyin bayan Tinubu ne da ke tallata neman takarar Osinbajo, ya yi wa Kwakwaso maraba zuwa APC.

Yin takara a PDP

Zabi na uku da ya rage wa Kwankwaso shi ne zamansa a PDP, a cwar majiya mai tushe.

Majiyar ta tabbatar mana cewa tuni shugabancin jam’iyyar na yankin Arewa maso Yamma ya sallama wa Kwankwasiyya kujerar Mataimakin Shguaban Kasa.

Da ma dai daga cikin dalilan da suka sa shi tunanin sauya sheka daga PDP shi ne takaddama game da bangaren da za a ba wa takarar mataimakin shugaban kasa.

“Yanzu wannan ya kau, shugabannin Arewa maso Yamma sun amince da dan takararmu.

“Ka san bangaren Aminu Wali ba shi da karfin fafatawa da mu, amma suna tunanin za su iya bugawa da mu idan na waje suka mara musu baya.

“Yanzu dukkansu sun amince da dan takararmu saboda sun gane cewa idan muka fice jam’iyyar saboda wannan shirmen, za su fi kowa asara.

“Shi ne suka ce, ‘Tunda dai kujerar Arewa maso Yamma kuke so, mun ba ku;’ Halin da ake ciki ke nan yanzu.

“Amma tsanaki da Allah, yana ci gaba da tuntuba; Duk ziyarce-ziyarcen ta’aziyya da ake kaiwa gidansa ba wani abu ba ne, siyasa ce.”

Amma wata majiya a Jam’iyyar PDP ta shaida wa Aminiya cewa ba a cim-ma matsaya ba tukuna.

Majiyar ta ce taron da aka yi na ranar Laraba ya amince a gudanar da zabe domin zaben Mataimakin Shugaban Jami’iyya na yankin Arewa maso Yamma.

“An jingine batun daidaitawa; Bangarorin biyu da suka fito daga Kano za su gwada farin jininsu a zaben da za a yi a lokacin taron da zai gudana a Kaduna,” inji shi.

‘Zaben Arewa maso Yamma muke jira’

Mun tuntubi shugaban bangaren Kwakwaso na Jam’iyyar PDP Reshen Jihar Kano, Shehu Sagagi, amma ya ce ba shi da masasniya game da wannan batu.

A cewarsa, abin da ya fi damun su shi ne ganin an yi taron jam’iyyar na yankin Arewa maso yamma wanda za’a gudanar a karshen mako mai zuwa a Kaduna.

Majiyoyi da dama da muka tuntuba sun shaida mana cewa tun da har shugabancin bagaren ya ki cewa uffan game da lamarin, babu wanda zai iya magana kwakkwara a kai face Kwamred Aminu Abdussalam Gwarzo, magana da yawun bangaren kuma makusancin Kwankwaso.

Kokarinmu na jin ta bakin Kwamraed Aminu Gwarzon ya ci tura, bai amsa kiran wayarmu ba, ko rubutaccen sakon da muka aika masa.

Mun kuma yi kokain jin ta bakin Babban Sakatare na Musamman ga Kwankwaso, Muhammad Mudathir Inuwa Ali, wanda shi ma kakakinsa ne, amma ko da muka kira shi a waya bai amsa ba.

Daga: Sagir Kano Saleh & Ismail Mudashir (Abuja), Clement A. Oloyede & Zahraddeen Yakubu Shuaibu (Kano).