✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Zan daina neman aikin gwamnati idan na samu N5m’

Ya ce in aka gan shi yana neman aiki bayan samun kudin a kona takardun shaifar karatunsa

Wani tsohon dalibin Jami’ar Maiduguri (UNIMAID) ya ce zai daina neman aikin gwamnati matukar ya samu  kyautar Naira miliyan biyar.

Tsohon dalibin, mai suna Galadima M. Kauji wanda ake wa lakabi da Musaddiq, ya bayyana cewa Naira miliyan biyar ta ishe shi ya kafa kasuwancin da ba sai ya nemi aikin gwamnati ba a rayuwarsa.

Matashin ya kara da cewa, idan har aka ba shi Naira miliyan biyar, daga baya aka gan shi yana neman aikin gwamnati, to a kona takardun shaidar kammala karatunsa.

Ya bayyana haka ne a Facebook, lokacin da yake tsokaci a kan wata tambayar da Aminiya ta yi a shafinta game da abin mutum zai yi idan ya samu Naira miliyan biyar.

Galadima ya ce, “Kasuwa zan fara da ita, shike nan na daina neman aikin gwamnati ke nan, wanda yake daidai da jiran gawon shanu.”