✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zulum zai tura dalibai kasar waje domin karatun aikin likita

A shirye-shiryen bude Asibitin Koyarwar Jami'ar Jihar Borno

Gwamnatin Jihar Borno za ta dauki nauyin dalibai ’yan asalin jihar zuwa kasar Masar domin yin karatun aikin likita.

Gwamnatin ta ce tura daliban su yi karatun digirin farko a fannin aikin likita da dangoginsa na daga cikin shirye-shiryenta na samar da isassun ma’aikata ga Asibitin Koyarwa na Jamia’ar Jihar.

Gwamna Babagana Umara Zulum ya umarci Ma’aikatar Ilimi, Kimiyya, Fasaha da Kirkira ta Jihar, ta zabo daliban da suka cancanta domin cin gajiyar shirin.

Ya ba da umarnin ne bayan karbar rahoton kwamitin da ya kafa kan kafa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Bonro da kuma Tsangayar Aikin Kiwon Lafiya na Jami’ar.

Ama bukatar kowanne daga cikin biyun kafin jami’ar ta samu izinin fara koyar da aikin likitanci.

Kwamintin, karkashin tsohon Shugaban Asibitin Koyarwa na Jamihar Maiduguri, Farfesa Othman Kyari, an dora masa alhakin fitar da tsare-tsaren da za a yi wa tsangayar da kuma asibitin.

Ya bayyana cewa za a gina asibitin mai gadaje 600 ne a matakai biyu; farko za a gina bangare mai cin gadaje 400, sannan a yi bangare mai cin gadaje 200.