✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An ci tarar kungiyoyin Firimiyar Ingila shida kan gasar Super League

Za a rage wa kungiyoyin maki 30-30 idan suka sake aikata hakan a gaba.

Hukumar Gudanar da gasar Firimiyar Ingila ta ce wasu manyan kungiyoyi shida da ke karkashinta za su biya tarar fam miliyan 22, sakamakon laifin da suka aikata na hada kai domin shirya kafa sabuwar  gasar Super League a nahiyar Turai.

Kungiyoyin shida da za a ci tararsu sun hada da Arsenal, Manchester United, Manchester City, Tottenham, Chelsea da kuma Liverpool.

Bayanan da Hukumar Firimiyar Ingila ta fitar sun ce dukkanin kungiyoyin sun amince da fuskantar hukuncin tilasta musu biyan tarar fam miliyan 25 da kuma ragewa kowaccensu maki 30-30, muddin suka sake aikata makamancin laifin na kokarin ballewa ko kafa wata sabuwar gasa a nan gaba.

Tun a watan Mayun da ya gabata ne Hukumar Kula da kKwallon Kafar nahiyar Turai, UEFA ta bayyana soma nazari kan daukar matakin hukunta kungiyoyin kwallon kafar da suka yi yunkurin kafa sabuwar gasar Super League, wadanda kuma har yanzu suka ki janye aniyar tasu duk da cikas din da ta gamu da shi.

Sashen Hausa na Rediyon Faransa RFI ya ruwaito cewa, da zarar UEFA ta cimma matsayar ladabtar da wadannan kungiyoyi, hukuncin ka iya zama haramta musu buga wasannin gasar cin kofin zakarun turai ko na Europa har na tsawon shekaru biyu.

A waccan lokacin UEFA ta bayyana samun nasarar tattaunawa da kungiyoyi 8 daga 12 da suka yi yunkurin kafa sabuwar gasar ta Super League, kan yiwuwar sassauta musu hukunci.

Ragowar kungiyoyi 4 da suka rage, Juventus, Barcelona, AC Milan da kuma Real Madrid kuwa na kan aniyar kafa sabuwar gasar, domin a cewar su takardun da suka gabatarwa hukumar FIFA da UEFA sun nuna neman izinin gudanar sabuwar gasar ce, ba wai son ballewa daga gasar cin kofin zakarun Turai ba.