✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kaddamar da kwamitin bincike kan rikicin sarautar Tangale a Gombe

A cewar Gwamna Yahaya, binciko dalilan da suka haifar da faruwar tashe-tashen hankulan ya zama wajibi

Gwamnan jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, a ranar Litinin ya kafa wani Kwamitin da zai binciko turka-turkar da ta mamaye nadin sarauta a Masarautar Tangale dake jihar.

Kwamitin dai wakilai 12 zai binciki musabbabin zanga-zangar da ta haifar da rikici a Karamar Hukumar Billiri dake jihar kan nadin sabon Mai Tangale.

Aminiya ta rawaito cewa, an sami wata zanga-zanga da tayar da tarzoma a cikin watan Fabrairun da ya gabata kan zabar sabon Sarkin yankin da ake kira da  Mai Tangale.

Tunda farko an dai an fara wata zanga-zanga data rikide ta zama tsrzoma har ta kai ga rasa rayukan wadanda basu ji ba ba su gani ba da ma asarar dukiyoyi masu yawa.

A cewar Gwamna Yahaya, binciko dalilan da suka haifar da faruwar tashe-tashen hankulan ya zama wajibi saboda yadda yamutsin ya nemi ya rikide ya zama na addini ko siyasa.

Mambobin kwamatin dai sun hada da Mai Shari’a Mahmud Gurama (Mai ritaya) a matsayin shugaba da da AIG Zubairu Muazu; Barista Mahmud Bappah Aliyu, Mista Sharon Faliya Cham, Rabaran Bitrus Urbanus Thaba da kuma Abdulhamid Salisu Bello.

Sauran mambobin kwamitin sun hada da Victoria Mamuda Usman da Barista Robert Wabida da Alhaji Abdullahi Jalo da kuma Dr Ya’u Ahmed Kashere.

Barista Musa Sa’idu be zai kasance Sakataren kwamitin, yayin da aka nada Barista H. N. Nwoye a matsayin mai ba da shawara.

Wakilinmu ya rawaito cewa kwamatin zai rika zama a harabar Babbar Kotun Jihar, kuma ana sa ran ya mika rahotonsa cikin kwanaki 60 masu zuwa.