✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An killace ’yan Najeriya 384 da aka kwaso daga Saudiyya a Abuja

Mutanen dai na cikin guda 802 din da aka tsare a wurare da dama na kasar

‘Yan Najeriya 384 da suka makale a kasar Saudiyya sun sauka a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe dake Abuja ranar Alhamis.

Mutanen dai na cikin guda 802 din da aka tsare a wurare da dama na kasar saboda shigarta ba bisa ka’ida ba.

Daga cikin mutanen dai akwai maza 300, mata 83 da kuma wani jariri, dukkansu kuma sun sauka a jirgin kasar Saudiyya mai lamba B773 da misalin karfe 1:10 na rana.

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya, Nwonye Ferdinand ya ce tuni aka mika mutanen ga Sansanin Alhazai na Babban Birnin Tarayya Abuja domin a killace su.

Hakan a cewar ma’aikatar ya dace da umarnin da Kwamitin Kar-ta-kwana da Shugaban Kasa ya Kafa kan yaki da cutar COVID-19 ya bukata.