✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An nada Buratai jakadan Najeriya a Benin

Buratai zai wakilci Najeriya a matsayin jakada a Jamhuriyyar Benin.

Shugaba  Muhammadu Buhari ya nada tsohon Babban Hafsan Sojin Kasan Najeriya, Laftanar-Janar Tukur Yusuf Buratai mai ritaya, a matsayin jakadan kasar a Jamhuriyyar Benin.

Yayin wani takaitaccen biki da aka gudanar a Abuja, Ministan Harkokin Waje, Geoffery Onyeama, ya gabatar da wasikun amince wa da tsaffin manyan hafsoshin sojin a matsayin jakadun Najeriya.

Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da jami’in watsa labarai na Ma’aikatar Harkokin Wajen, Mista Kimiebi Ebeinfa ya fitar a ranar Talata.

Sanarwar ta ce an kuma mika wa tsohon Hafsan Hafsoshin Najeriya, Janar Abayomi Gabriel Olanisakin takardar amincewa da shi a matsayin jakadan Najeriya zuwa kasar Kamaru.

Ana iya tuna cewa, tun a watan Fabrairun da ya gabata ne Shugaba Buhari ya gabatar da sunayen tsaffin manyan hafsoshin sojin da ya sauke ga Majalisar Dattawa domin amincewa da su a matsayin Jakadun kasar.

Cikin wasikar da Shugaba Buhari ya aike wa da Majalisar tun a wancan lokaci, ya bayyana sunaan Janar Abayomi Olanisakin, Laftanar-Janar Tukur Yusuf Buratai, Rear Admiral Ibok-Ete Ekwe Ibas, Air Marshal Sadique Abubakar da kuma Air Marshal Mohammed Usman a matsayin Jakadu.

Sai dai a yanzu sanarwar da Ma’aikatar Harkokin Wajen ta fitar ba ta fayyace kasashen da za a tura sauran manyan hafsohin Jakadanci ba.