✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba zan lamunci wata kungiya ta kawo hargitsi a Najeriya ba — Buhari

Babu wata kungiya ta addini ko kabila da zan bari ta kawo hargitsi a kasar nan.

Shugaba Muhammadu Buhari ya sha alwashin bayar da kariya ga dukkanin kabilu da addinai a kasar nan ba tare da la’akari da karanci ko yawansu a kowane yanki na kasar ba.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar Mallam Garba Shehu ya fitar a ranar Lahadi, ta ce Shugaban kasar ya yi martani gami da Allah wadai dangane wasu rahotanni na rikicin kabilanci a wasu sassa na kasar.

Sanarwar ta ce shugaban kasar yana gargadin ire-iren wadannan kungiyoyi da cewa gwamnatinsa ba za ta zuba musu idanu su ci gaba da rura wutar kiyayya da tashin hankali a tsakanin junansu ba.

Sanarwar ta ce, “Shugaba Muhammadu Buhari  ya ce gwamnatinsa kamar yadda kundin tsarin mulkin kasa ya yi tanadi, za ta kare dukkan mabiya addinai da kuma kabilun kasar ko da kuwa suna da rinjaye ko ’yan tsiraru ne su a yankin da suke rayuwa.”

“Shugaban kasar yana kuma martani kan rahotannin barkewar rikici a wasu sassan kasar wanda wasu kungiyoyi da ke da alaka da kabilanci ko bangarancin addini suke haddasawa.”

“Ya yi Allah wadai da irin wannan tashin hankali tare da bayar da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta dauki matakan da suka dace don dakile yaduwar duk wani rikici.”

“A karshe sanarwar tana cewa, Shugaban kasar ya bukaci malaman addinai, da sarakunan gargajiya da gwamnoni da sauran shugabannin siyasa da na al’umma da su hada hannu da gwamnatin tarayya, domin tabbatar da al’ummomin da ke yankunansu bas u wargaje ba saboda dalilai na bambancin kabila ko addini ba.”

Aminiya ta ruwaito cewa a kwanan nan ne rikicin kabilanci ya auku a birnin Ibadan a Jihar Oyo da ke Kudu maso Yammacin Najeriya, inda aka tabbatar da salwantar rayukan mutane da dama a mummunar arangamar da ta auku a tsakanin kabilar Hausawa da Yarbawa.