✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Bayan lashe kofi 25, Marcelo zai bar Real Madrid

Marcelo ya shafe shekara 15 a Real Madrid, inda ya lashe kofi 26.

Dan wasan baya kuma Kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Marcelo, ya sanar cewa lokacinsa ya zo karshe a kungiyar.

Dan wasan ya bayyana haka ne a daren ranar Asabar, bayan da kungiyarsa ta doke Liverpool da ci daya mai ban haushi a wasan karshe na Gasar Zakarun Turai.

Marcelo ya shafe tsawon shekara 15 yana murza leda a Real Madrid, tun bayan da kungiyar ta saye shi a 2007.

Kyaftin din ya zama dan wasa mafi shahara a kungiyar bayan da ya lashe kofi 25, ciki har da kofin Zakarun Turai guda biyar.

Dan wasan bayan wanda dan asalin kasar Brazil ne, ya fara hada kayansa don neman sabuwar kungiyar da za su kulla yarjejeniya don komawa da buga kwallo.

Kwantaragin Marcelo zai kare a karshen watan Yuli, kuma tuni ya zauna da masu ruwa da tsakin kungiyar don sanin makomarsa.