✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Da wuya a shawo kan cutar Coronavirus a bana – WHO

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce da wuya a iya samun nasarar murkushe annobar Coronavirus a bana. Daraktan Hukumar na sashen shirin bayar da…

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce da wuya a iya samun nasarar murkushe annobar Coronavirus a bana.

Daraktan Hukumar na sashen shirin bayar da agajin lafiya na gaggawa, Michael Ryan ne ya bayyana hakan yayin zantawarsa da manema labarai a ranar Talata.

“Ina ganin za mu yi gaggawar yanke hukunci muddin muka fara tunanin murkushe kwayoyin cutar zuwa karshen shekarar nan da muke ciki.”

“Abin da kawai za mu iya bayar da tabbaci a kai wanda shi ma sai mun mayar da hankali shi ne yaduwar cutar, mace-mace da sauran bala’o’in da suka danganci cutar.”

Mista Ryan ya ce a yanzu abin da Hukumar WHO ta fi mayar da hankali a kai shi ne aiwatar da duk wata mai yiwuwa wajen rage yaduwar cutar gwargwadon iko da kuma yawaita yi wa mutane allurar rigakafin cutar.

A cewarsa,duk da kalubalen da Hukumar Lafiya ta ke fuskanta, a halin yanzu akwai ci gaba da aka samu wajen rarraba allurar rigakafin cutar idan aka kwatanta da yanayin da ake ciki makonni goma da suka gabata.

“Idan allurar rigakafin ta fara tasiri a kan takaita mace-mace da kwantar da mutane a asibiti sakamakon kamuwa da cutar, to babu shakka tasirin da za a samu wajen dakile yaduwarta zai ba mu damar shawo kanta cikin gaggawa,” in ji Mista Ryan.