✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ganduje na son yi wa asusun Kano karkaf —PDP

Wannan ya nuna karara cewa gwamna na kashe kudaden ba tare da wata ka’ida ba.

Babbar Jam’iyyar adawa a Kano ta PDP ta bayyan damuwa kan yadda Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ke neman yi wa asusun jihar karkaf.

Wannan kuwa ya biyo bayan sanarwar da ya yi cewa zai kashe naira miliyan 500 domin kawata gadar Kofar Ruwa da aka sanya wa sunan marigayi Galadiman Kano, Tijjani Hashim.

Cikin wata sanarwa da shugaban PDP Shehu Wada Sagagi ya fitar ta ce, kudin da aka amince a kashe ya yi yawa, kawai ana son a barnatar da dukiyar al’umma ne.

Sanarwar ta ce an gano cewa an fara aikin ne makonni gabanin a amince da kashe kudin kuma baya cikin kashe-kashen kudin da aka tsara yi a 2022 ballantana 2021.

“Wannan laifi ne da zai iya janyo mutum ya bar ofishinsa, bin damuwa ne matuka da ya kamata a sanya wa ido da a ce Jihar Kano tana da jajirtattun ’yan majalisar dokoki.

“Muna kira ga kungiyoyin fararen hula da hukumomin hana cin hanci da rashawa irinsu EFCC da ICPC su sanya ido domin tabbatar da bin diddigi da zai tabbatar da kyakkyawan shugabanci.”

“Wannan ya nuna karara cewa gwamna na kashe kudaden ba tare da wata ka’ida ba, wanda hakan zai iya janyo tabarbarewar tattalin arzikin jihar gabanin karewar wa’adinsa na biyu, ya kuma yi wa asusun jihar karkaf.”

Sanarwar ta kara da cewa, “a matsayinmu na jamiyyar adawa, muna kira ga Majalisar Dokokin Jihar da sauran masu ruwa da tsaki da su yi watsi da wannan lamari domin kuwa hakan ba daidai ba ne la’akari da yadda tattalin arzikin jihar ya yi nukusani.”