✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ganduje ya bayyana dabarar magance rikicin makiyaya da manoma

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano, ya nemi a samar da wata doka da za ta haramta zirga-zigar shanu daga Arewa zuwa Kudancin Najeriya.…

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano, ya nemi a samar da wata doka da za ta haramta zirga-zigar shanu daga Arewa zuwa Kudancin Najeriya.

Ganduje ya yi wannan kira ne a ranar Lahadi yayin zanta wa da manema labarai a garin Daura da ke Jihar Katsina.

A cewarsa, ta hanyar haramta zirga-zirgar shanu daga Arewa zuwa wasu sassan kasar ne kadai za a kawo karshen rikice-rikicen makiyaya da manoma.

Gwamnan ya ce rikice-rikicen manoma da makiyaya ba zai kare ba har sai an yi dokar haramta zirga-zirgar shanu daga Arewa zuwa yankin tsakiyar kasar wato Middle Belt da sauran yankunan Kudancin kasar nan.

Ya ce za a magance matsalar satar shanu da rikice-rikicen da ke faruwa tsakanin manoma da makiyaya a yayin da aka fara aiki da irin wannan doka.

“Matukar ba a dakatar da zirga-zirgar shanu tsakanin yankunan biyu ba, to ba za a taba kawo karshen rikicin manoma da Fulani makiyaya ba,” inji Ganduje.

Gwamnan ya ce gwamnatinsa ta dakile fitintunun ’yan fashin daji da sauran ayyukan ta’addanci ta hanyar samar da wuraren kiwo ga makiyaya a wani jeji da ke kusa iyakar Jihar Kano da Katsina.

“Muna ci gaba da gina Ruga a dajin Samsosua da ke kan iyakarmu da Katsina kuma mun samu gagarumar nasar wajen dakile ayyukan ’yan fashin daji a yankin,” a cewar Ganduje.

“Saboda haka muna gina gidaje da dama da madatsun ruwa dannan muna kokarin kafa wata cibiyar dashen mahaifa ta dabbobi da kuma asibitinsu duk saboda cin moriyar makiyaya a yankin.”

Ganduje yayin tsokaci dangane da nadin sabbin manyan hafsoshin soji da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi, ya ce yana sa ran za su yi aiki tare da Gwamnonin Jihohi da suka san bukatun al’ummarsu domin mai daki shi ya san inda ruwa ke yi masa yoyo.

Kazalika, takwaransa na Jihar Gombe, Inuwa Yahaya, ya shawarci sabbin manyan hafsoshin soji da su dage wajen cika burace-burace ta tsammanin da ’yan Najeriya ke yi a kansu.

Sauran gwamnonin jam’iyyar APC da suka kai wa Shugaba Buhari ziyara garin Daura tare da Gwamna Ganduje sun hada da na Jigawa Muhammadu Badaru Abubakar, da Atiku Bagudu na jihar Kebbi.

Aminiya ta ruwaito cewa a ranar Asabar ne Shugaban Kasa Buhari ya sabunta rajista a jam’iyyarsa ta APC a mazabarsa ta Dakin Yara da ke garin Daura a Jihar Katsina.