✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ganduje ya tsawaita wa’adin hutun dalibai a Kano

An bukaci iyaye da su tabbatar ’ya’yansu sun koma makaranta a ranakun da aka kayyade.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya kara wa’adin mako daya kan hutun dalibai na makarantun Firamare da Sakandire a fadin Jihar Kano.

Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da Kwamishinan Ilimin Jihar, Muhammad Sanusi Kiru ya fitar a ranar Litinin.

Sanarwar mai dauke da sa hannun mai magana da yawun Kwamishinan, Aliyu Yusuf, ta ce tsawaita hutun ya biyo bayan yunkurin da Gwamnatin Jihar ke yi na daidaita jadawalin karatu a fadin jihar.

Kazalika, ya ce matakin hakan ya biyo sauye-sauye da annobar Coronavirus ta kawo a jadawalin karatu da aka tsara kafin bullar annobar.

Sanarwar ta ce a yanzu daliban makarantun kwana za su koma a ranar Lahadi, 12 ga watan Satumba, yayin da ’yan jeka-ka-dawo za su koma a ranar Litinin, 13 ga watan na Satumba.

“Ana umartar daliban da ke makarantun kwana su koma a ranar 12 ga watan Satumba 2021 maimakon 5 ga wata, sannan ’yan jeka-ka-dawo su koma ranar Litinin 13 ga watan Satumba 2021 maimakon 6 ga wata,” a cewar sanarwar.

Kwamishinan ya kuma yaba wa iyayen dalibai dangane da goyon bayan da suka bai wa Ma’aikatar Ilimi da kuma Gwamnatin Jihar Kano yana mai fatan za su dore a kan haka.

Ya kuma bukaci iyaye da su tabbatar ’ya’yansu sun koma makaranta a wannan ranaku da aka kayyade.