✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gaskiyar boren sojoji kan yaki da Boko Haram

An yi karin gishiri a labarin duk da cewa ba yanzu farau ba

Aminiya ta bincike aikin abin da ya faru bayan samun labarin bore da wasu sojoji karkashin Runduna ta 7 ta Sojin Kasan ta Najeriya suka yi kan yaki da Boko Haram.

Majijoyinmu a Barikin Sojoji na Maimalari da ke Maiduguri, Jihar Borno sun bayyana abin da ya faru, da kuma karin gishiri da aka yi a labarin.

Da farko rahotannin sun nuna cewa wasu sojoji da taka tura yaki da kungiyar Boko Haram sun karci kasa suna ta luguden wuta a gaban hedikwatar rundunar Operation Lafiya Dole da ke barikin, cewa sai dole an biya su alawus din da suke bi, an kuma ba su isassun kayan yaki na zamani.

cewaan samu hatsaniya a Barikin Sojoji na Maimalari da ke Maiduguri, bayan korafin da wasu sojoji suka yi  kan turasu fagen fama amma basu da wadatattun makamai na zamani.

An ruwaito cuewa sojojin da aka tura a rukuni na 2 na Operation Tura Ta Kai Bango, karkashin kulawar Operation Lafiya Dole sun yi tirjiyar ce bayan an sake tura su garin Bama.

Rukunin farkon shi ne ke aikin karkade ’yan kungoyar Boko Haram a yankin dajin Sambisa da kuma tafkin chadi, kamar yadda wata majiya a barikin sojan na Maimalari ta shaida wa Aminiya.

Wani Soja da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewar hakika an yi bore a gaban hedikwatar Operation Lafiya Dole da ke barikin, amma batun yin harbe-harbe ba gaskiya ba ne.

“Yan uwanmu sojoji sun yi bore domin ba su kayan aiki, da kuma ba su hakkokinsu, saboda makaman da ’yan Boko Haram suke amfani da su mu bamu da su.

“Shi ya sa duk lokacin da suka kawo mana hari ba a kwashewa da dadi; ko harin da suka kawo na kama garin Dikwa sun yi mana barna, saboda makamansu sun fi namu,” a sojan.

Wani ma’aikaci farar hula a cikin barikin da yaki amincewa a nadi muryarsa, ya tabbatar da aukuwar zanga-zangar da sojojin suka yi a hedikwatar Operation Lafiya Dole.

Sai dai ya ce, “Maganar gaskiya ba ji wani harbi ba, amma dai sun taru a kofar ofishin don gabatar da kokensu.

 

Ba yanzu farau ba

“Kuma mu da muke cikin bariki ai ba yau hakan ta fara faruwa ba, amma dai yadda na ji ana ta zuzuta batun gaskiya bai kai hakan ba.

“Fatarmu dai su manyan su taimaka su biya su hakkokin nasu, kuma a samar musu da kayan yaki isassu, da ana yin hakan ai ina ganin da yanzu lamarin Boko Haram ya zama tarihi.”

Wani tsohon Soja da Aminiya tuntuba, ya ce maganar gaskiya a yadda ya san sojojin Najeriya, da ana ba su kayan aiki da duk wani ta’adanci ya kau a kasar.

“Ganin yadda suka je wasu kasashe suka samar da zaman lafiya, amma ace a nan gida yaki da wata kungiya wai ya gagare su, kai ma kasan akwai lauje cikin nadi,” a cewar Baba Ali Tsohon Soja.

Game da zanga-zangar sojojin saboda rashin isassun makamai, ya ce, “Ai ba yau aka fara irin hakan ba, wani lokaci a kan rashin biyan su hakkokinsu, rashin makamai na zamani da sauran abubuwa; Don haka ni ba na mamaki don na ji wai kananan sojoji sun yi bore.

“A bincika, akwai dalilin da ya sa hakan, ai mu a lokacinmu umarni ne, kawai dole a bi, sabanin yanzu da wai har soja zai bijire wa umarnin shugabansa, sai dai Allah ya kyauta.”

Aminiya ta yi kokarin jin ta bakin Kanar Ado Isa, mai magana da yawun Rundunar Operation Lafiya Dole, amma wayarsa ba ta shiga, kai hatta sakon karta kwana ya ki tafiya.

Amma gidan Talabijin na Channels ya ruwaito shi yana tabbatar da labarin.

Zanga-zangar sojojin na zuwa ne ba a dade ba bayan Mashawarcin Shugaban Kasa kan Tsaro, Babagana Munguno ya yi zargin cewa an wawure kudin sayen makaman karfafa yaki da Boko Haram da aka bayar karkashin tsoffin Hafsoshin Tsaro.

Amma mai magana da yawun Shugaban Kasa, Garba Shehu, ya bayyana cewa ba zai yiwu a yi kwanciyar magirbi a kan kudin makamai a karkashin Shugaba Muhammadu Buhari.