✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gwamnan Bauchi ya yi barazanar ficewa daga kwamitin yakin neman zaben Atiku

Hakan dai zai iya tsananta rikicin cikin gidan PDP

Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya yi barazanar ficewa daga Kwamitin Yakin Neman Zaben dan takarar Shugaban Kasa a Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, saboda mugun halin da ya ce ana nuna masa.

Tuni Gwamnan ya aika wa Shugaban PDP na Kasa, Iyorchia Ayu, da wasika mai dauke da kwanan watan uku ga watan Nuwamba don bayyana masa halin da yake ciki.

Samun wasikar ke da wuya shugaban jam’iyyar na kasa ya jagoranci tawaga ta musamman da ta kunshi Gwamnan Sakkwato, Aminu Tambuwal da tsohon Gwamnan Jigawa, Sule Lamido zuwa wajen Gwamnan.

Da alama barazanar da Bala ya yi ta tsananta rikicin cikin gidan da jam’iyyar ke fama da shi.

Lamarin dai ya sanya Gwamnonin PDP biyar da suke ganin ba a yi musu daidai ba, da suka hada da Nyesom Wike na Ribas da Okezie Ifeanyi Ugwuanyi na Inugu da Samuel Ortom na Binuwai da kuma Seyi Makinde na Oyo, suka ci gaba da hada kai don su yaki Abubakar da Shugaban jam’iyyar na kasa, Iyorchia Ayu.

Cikin wasikar da Bala ya rubuta wadda jaridar Daily Nigerian ta rawaito ta samu ganinta, Gwamnan ya zargi tsohon Mataimakin Shugaban Kasar da hada kai ’yan “Bala Must go” masu son ganin bai koma mulki a wa’adi na biyu ba.

Bala ya bayyana a cikin wasikar cewa, daga cikin ’yan yekuwar ta “Bala Must go” har da na hannun daman Atiku, Bello Kirfi, da tsohon Gwamnan jihar, Adamu Mu’azu da kuma tsohon Shugaban Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara.