✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Harin kunar bakin wake ya kashe mutum 10 a Somaliya

Wani harin kunar bakin wake na ranar Juma’a da aka kai filin wasan kwallon kafa da ke garin Galkayo a kasar Somaliya ya kashe mutum…

Wani harin kunar bakin wake na ranar Juma’a da aka kai filin wasan kwallon kafa da ke garin Galkayo a kasar Somaliya ya kashe mutum 10 inda kuma da dama suka jikkata kamar yadda hukumomin kasar suka tabbatar.

Da ya ke zantawa da kamfanin dillancin labarai na Anadolu, Ali Hussein, wani jami’in dan sanda a yankin Galmudug ya tabbatar da cewa dan kunar bakin wake ne ya kai harin.

Ali Hussein ya ce daga cikin wadanda harin ya ritsa da su akwai wasu manyan dakarun sojin kasar bakwai, kuma da yiwuwar adadin wadanda suka mutu ya karu a yayin da ake ci gaba da bincike.

Harin ya faru ne gabanin Firaiminista Mohammed Hussein Roble da shugaban yankin na Galmadug, Ahmed Abdi Kariye suka gabatar da jawabansu da aka tsara.

Dan kunar bakin waken ya auna jami’an gwamnati da ’yan tawagar tsaro ta Firaiministan da ke kan hanyar zuwa filin wasan domin taron magoya bayan gwamnati.

Kazalika, shugaban hafsan sojan kasa na Somaliya, Odawa Yusuf Rageh ya tabbatar da aukuwar harin.

Rageh ya ce daga cikin manyan dakarun soji da harin ya ritsa da su akwai Janar Abdi Asics Abdullahi Qooje, Kanal Mukhtar Abdi Adan da sauran manyan jami’an gwamnati.

Daga bisani kungiyar Al Shabab da ke tayar da kayar baya a yankin ta dauki alhakin kai harin.