✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Hatsarin mota ya yi ajalin mutum 8 a hanyar Bauchi

Hatsarin ya faru ne bayan wata karamar mota ta yi karo da tifa a hanyar Dass zuwa Bauchi.

Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa (FRSC) ta tabbatar da rasuwar mutum takwas a wani hatsarin mota a cikin dare a Jihar Bauchi.

Kwamandan FRSC na Jihar Bauchi, Yusuf Abdullahi, ya ce hatsarin ya faru ne bayan wata karamar mota — Opel Vectra — ta yi karo da wata tifa kirar Marsandi.

Yusuf, ya ce mata biyu da maza shida, ciki har da karamin yaro ne suka rasu, direban tifar kadai ne ya tsira a hatsarin.

Ya ce hatsarin ya auku ne a kauyen Koltukurwa da ke kan hanyar Dass zuwa Bauchi da misalin karfe 9.30 na dare, ranar Asabar.

Ya bayyana cewa an ajiye gawarwakin a Babban Asibitin Dass, sannan ya alakanta hatsarin da gudu da kuma daukar kaya fiye da kima.

Don haka ya yi kira ga masu ababen hawa da su rika kiyaye dokokin hanya a kowane lokaci.