✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jarumin Kannywood, Sani SK, ya rasu

Ya rasu ne bayan fama da jinya.

Allah Ya yi wa jarumin masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood, Sani Garba SK rasuwa bayan fama da jinya da ya yi na tsawon lokaci.

Darakta Aminu S. Bono ne ya sanar da hakan, inda ya wallafa a shafinsa na Instagram cewa, “Inna lillahi wa inna ilai rajiuna. Sani Garba SK, Allah Ya gafarta maka.”

Aminiya ta ruwaito a watan Yulin bana cewa jarumin yana neman taimako domin jinyar rashin lafiyar da yake yi.

A wani bidiyo da Aminiya ta gani na Sani SK a lokacin ya ce yana matukar bukatar taimakon ne domin kula da lafiyarsa.

Jarumin ya tabbatar da cewa an taimaka masa, sai dai yana bukatar karin taimako, hakan ne kuma ya sa ya yi bidiyo domin a ga halin da yake ciki.

Jim kadan bayan bidiyon ya fito, wasu mutane suka fara caccakar ’yan Kannywood cewa ba sa taimakon junansu.

Sai dai a lokacin Fauziyya D. Suleiman, fitacciyar marubuciya wadda kuma ta yi fice wajen taimakon jama’a a ciki da wajen Kannywood, ta ce jarumin yana bukatar taimako, ta kuma yi kira a taimaka don Allah ba tare da cin mutuncin ’yan Kannywood ba.

A cewarta, “Tun da Sani SK ya saki bidiyon nan mutane ke ta tambayar lambar waya da asusun bankinsa, don haka na kira shi ya turo da kansa.

“Amma abin da na ke so mutane su gane,  SK ya jima yana jinya; na san wani daga irin taimakon da abokan sana’arsa suka ba shi.

“Kai, hatta ta sanadiyyata mutane da yawa sun taimaka masa, mu ma mun sha saya masa magani, sannan mun biya wa yaransa su biyu kudin makaranta.”

Haka kuma a watan jiya, wato Nuwamban bana, Aminiya ta ruwaito yadda ‘yan Kannywood din suka tara wa marigayin sama da Naira miliyan a cikin kwana daya.

Da take jawabi kan kudin da aka tara masa a watan na jiya, Fauziyya D. Suleiman ta ce Abdul Amart Mai Kwashewa ya ba shi Naira dubu 500. Hadiza Gabon ta ba shi Naira dubu 250, Ali Nuhu ya ba shi Naira dubu 100. Aliyu Tsamiya ma ta ba shi Naira dubu 100, sannan wasu da yawa ma sun bayar da gudummawarsu daga masana’antar ta Kannywood.

An ta yi rade-radin jarumin na barkwanci ya rasu, inda ko a watan jiya sai irin wannan rade-radin ya fito kafin marigayin da kansa ya fito ya karyata.