✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Jirgin ruwa ya nitse da mutum 17 a tekun Rasha

An kasa tura jirgin sama domin ceto su, sakamakon matsalar yanayi da ake yi a kasar.

Mutane 17 sun bace yayin da aka ceto wasu biyu bayan da wani jirgin ruwan kamun kifi ya nitse da su a Tekun Barents dake kasar Rasha.

Kafafen watsa labaran kasar sun ruwaito cewar lamarin ya faru ne a ranar Litinin.

Rahotanni sun ce jirgin ruwan mai lakabin ‘Onega’ ya nitse ne a kusa da tsibirin Novoya Zemlya dauke da mutane 19 a ciki.

Tuni dai rahotanni suka ce Ma’aikatar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasar ta bazama domin ceto wanda suka nitse a ruwan.

Ma’aikatar ta danganta faruwar lamarin da yawaitar dusar kankara da jirgin ruwan ya tarar.

Yanzu haka dai ana ci gaba da kokarin ceto mutanen, sai dai an gaza tura jirgin sama saboda matsalar yanayi da ake ciki.