✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

KEDCO ya taya sabon Sarkin Dutse murnar darewa kan karaga

Tawagar kamfanin ce ta kai wa Sarkin ziyara a fafatawa ranar Talata

Hukumar gudanarwar Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Shiyyar Kano (KEDCO) ya taya Hameem Nuhu Sunusi murnar zama sabon Sarkin Dutse da ke Jihar Jigawa.

Sabon Sarkin ya dare kan karagar mulkin ne bayan rasuwar mahaifinsa, Nuhu Muhammad Sanusi.

Shugaban kamfanin, Ahmed Dangana ne ya jagoranci tawagar kamfanin don taya Sarkin da gwamnati da ma al’ummar Jihar murna ranar Talata a fadar basaraken, kamar yadda Shugaban Sashen Sadarwa na KEDCO, Sani Bala Sani ya fada a cikin wata sanarwa ranar Alhamis.

Da yake jawabi a fadar Sarkin, Ahmed Dangana, ya yi addu’ar Allah Ya ba sabon sarkin damar dorawa daga inda mahaifinsa ya tsaya wajen ciyar da Jihar da ma masarautar.

Da yake mayar da jawabi, Sarkin na Dutse ya gode wa Shugaban da ziyarar da kuma fatan alherin, inda ya yi addu’ar dorewar dangantaka tsakanin masarautar da kamfanin.

Ya kuma yaba wa kamfanin na KEDCO saboda samun ingantuwar wutar lantarki a birnin na Dutse da ma Jihar ta Jigawa.