✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

Mutum 15 sun rasu a hatsarin kwalekwale

Wasu da dama sun bace, a yayin da wasu 17 suka tsallake rijiya da baya.

Mutum 15 sun rasu, wasu da dama kuma sun bace sakamakon hatsarin kwalekwale gabanin shan ruwa a Jihar Neja.

Mutum 17 kuma sun tsallake rijiya a hatsarin kwalekwalen da ya auku da magaribar ranar Asabar a yayin da mutanen ke hanyar komawa gida bayan cin kasuwa.

Hatsarin ya ritsa da mutanen ne bayan sun baro Kasuwar Zumba a  Karamar Hukumar Shiroro za su koma gidajensu a Tijana da ke Karamar Hukumar Munya, Jihar Neja.

Sarkin Kasuwan Zumba, Malam Adamu Ahmed ya ce kwalekwalen na dauke da mutun 60 da suka hada da mata da kanana yara a lokacin da ya kife sakamakon iska mai karfi.

Ya cewa wasu daga cikin mutanen na hanyarsu ta komawa gidajensu da suka kaurace wa ne a kwanakin baya saboda hare-haren ’yan bindiga.

Malam Adamu ya ce masu ninkaya sun yi nasarar ceto mutum 17 a raye, kasancewar ba a jima da faruwar lamarin ba aka sanar da su.

Suna kuma ci gaba da kokarin ceto mutanen da ba a gani ba, duk da cewa ana ruwan sama kamar da bakin kwarya a lokacin da muke kammala hada wannan rahoto.

A shekarar 2017, kifewar wani kwalekwale ya lakume rayuka 13 daga cikin fasinjojinsa mutum 30 a hanyarsu ta komawa gida daga kasuwar ta Zumba.