Orubebe ya fice daga PDP, ya ce jam’iyyar ba ta shirya karbar mulki daga APC ba | Aminiya

Orubebe ya fice daga PDP, ya ce jam’iyyar ba ta shirya karbar mulki daga APC ba

Godsday Orubebe
Godsday Orubebe
    Sani Ibrahim Paki

Tsohon Ministan Neja Delta, zamanin tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan, Godsday Orubebe, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar PDP.

A wata wasika da ya aike wa Shugaban jam’iyyar na kasa, Iyorchia Ayu, dauke da kwanan watan 20 watan Yunin 2022, Orubebe ya ce ficewar ta fara aiki ne nan take, kuma ya aike da kwafin wasikar ga Shugaban jam’iyyar na mazabarsa da ke Karamar Hukumar Burutu da ke Jihar Delta.

Ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda PDP ta ki amfani da tsarin karba-karba wajen fitar da dan takararta na Shugaban Kasa, inda ya ce jam’iyyar ba ta shirya sake karbar mulki daga APC ba a 2023.

Wasikar ta ce, “A cikin wannan wasikar, ina sanar da kai aniyata ta janyewa daga dukkan harkokin jam’iyya a matakin mazaba da Karamar Hukuma da Jiha da kuma kasa baki daya.

“Ina godiya da damar da na samu ta kasancewa cikin jam’iyyar da ta kawo wa Najeriya gagaumin sauyi na ci gaba.

“Lokacin da muka fadi zaben Shugaban Kasa na 2015, na yi tsammanin jam’iyyar za ta yi nazari na tsanaki kan hanyar da za ta sake karbar mulki cikin kankanin lokaci.

“Sai dai yanayin da muke ciki a yanzu bai nuna wani shiri da jam’iyyar ke kokarin yi na sake karbar mulki a 2023 ba.

“Matakin da PDP ta dauka na barin takarar Shugaban Kasa a bude, ta inda har dan Arewa ya sami nasara watsi ne da Tsarin Mulkinta.

“Hakan ya sa manyan mukaman jam’iyyar guda biyu na Shugaban Kasa da Shugaban jam’iyya a hannun ’yan Arewa, wannan ya saba da sashe na 7.3 (0) na Kundin Tsarin Mulkin jam’iyyar,” inji shi.

Tsohon Ministan ya kuma jinjina wa Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike kan irin yadda ya fafata a zaben fitar da gwanin jam’iyyar, inda ya ce tarihi ba zai manta da shi ba.

Sunan Orubebe dai ya fara tambari ne lokacin da ya yi kokarin hargitsa wajen da ake tattara sakamakon zaben Shugaban Kasa a Abuja a shekarar 2015.