✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sergio Ramos ya koma PSG

Ramos ya sanya hannun zama a PSG har zuwa 2023.

Kungiyar kwallon kafa ta Paris-Saint Germain ta dauki Sergio Ramos a matsayin sabon dan wasanta.

Kungiyar ta PSG ta cimma yarjejeniyar shekara biyu da Ramos, zuwa karshen kakar wasanni ta 2023.

  1. EFCC na neman hadimin Tambuwal kan damfarar N2.2m
  2. Mun aika ‘yan ta’adda da yawa lahira —Hafsan Sojin Kasa

Tsohon kyaftin din na Real Madrid ya sauya shekar ne zuwa PSG bayan karewar kwantaraginsa da kungiyar a karshen watan Yuni, 2021.

Ramos ya shafe shekara 16 a Real Madrid kafin daga bisani ya raba gari da ita.

Dan wasan mai shekara 35 a duniya ya buga wa Madrid wasanni 671 sannan ya zura kwallaye 101, tare da lashe kofi 22 da kungiyar.