✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaban Chadi ya ziyarci Buhari a Abuja

Shugaba Deby ya shafe shekaru fiye da 30 a karagar mulkin kasar Chadi.

Shugaba Idris Deby na Kasar Chadi, ya gana da takwaransa na Najeriya Shugaba Muhammadu Buhari kan batutuwan da suka shafi kasashen biyu.

Ganawar na zuwa ne ranar Asabar yayin da Shugaba Deby ya ziyarci Buhari a fadarsa ta Villa da ke birnin Abuja.

Shugaba Deby ya shafe shekaru fiye da 30 a karagar mulkin kasar Chadi, inda a halin yana daya daga cikin ’yan takara na zabe kasar da za a yi ranar 11 ga watan Afrilun 2021.

A yayin da sanarwar da Fadar Shugaban Najeriya ta fitar ba ta yi bayani ba game da hakikanin batutuwan da shugabannin suka tattauna, sai dai ganawar na zuwa ne a daidai lokacin da Najeriya, Kamaru, Chadi, da Nijar ke fuskantar karuwar hare-haren mayakan Boko Haram.

Aminiya ta ruwaito cewa, a makon jiya ne wasu ’yan bindiga da ake zargin mayakan Boko Haram ne suka kai hari wani kauye da ke yankin Arewa Mai Nisa a Kasar Kamaru wanda ya salwantar da rayukan mutum uku ciki har da mata biyu.

Wannan hari na zuwa ne a daidai lokacin da makamancinsa ya auku wanda mayakan Boko Haram suka kai garin Wulgo a Najeriya har ya yi ajalin wasu sojojin Kamaru guda biyu.

Kazalika, a tsawon makonni biyu da suka gabata, hare-hare ta’addanci sun yi sanadiyar hallaka mutane sama da 200 a jamhuriyyar Nijar.