✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Taron PDP: Tambuwal ya janye daga neman takarar shugaban kasa

Ya ce ya janye ne domin mara wa tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, baya.

Gwamnan Jihar Sakkwato, ya janye daga neman takarar kujerar shugaban kasa a jam’iyyar PDP.

Ya sanar da haka ne a yayin da ake tsaka da babban taron jam’iyyar domin zaben dan takarar da zai daga tutar jamiyyar a zaben 2023.

“Ni, Aminu Tambuwal, bayan tattaunawa da mutane daga kowane yanki na kasar nan, na yanke shawarar janye neman takarata,” kamar yadda ya sanar a wurin taron.

Ya ce ya janye ne domin goyon bayan takarar tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, kuma ya bukaci magoya bayansa da su mara wa Atiku baya.

Sanarwar tasa ke da wuya, wurin taron ya cika da tafi da kuma yi mishi fatan alheri.

Kawo yanzu, gwamnan shi ne mutum na uku da ya janye daga neman takarar a ranar zaben.

Tun da farko, an wayi gari da labarin janyewar Mohammed Hayatu-Deen, kafin daga bisani Dokta Anakweze ya sanar da janyewarsa domin mara wa Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, baya.

Zuwa yanzu mutum 11 ke nan ke fafatawa a zawarcin tikitin na PDP.