✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tsohon Mataimakin Gwamnan Kaduna ya mutu

El-Rufai ya ce ya yi rashin aboki.

Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Kaduna, Yusuf Barnabas Bala wanda aka fi sani da Bantex, ya riga mu gidan gaskiya.

Aminiya ta samu cewa Bantex ya amsa kiran Mahaliccinsa da safiyar ranar Lahadi.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Gwamnan Jihar, Malam Nasir El-Rufai a wata sanarwa da ya fitar ya ce ya yi rashin aboki wanda ya zame masa dan uwa.

“Cike da alhini da takaici, na samu labarin mutuwar aboki na kuma dan uwa, Mai girma Barnabas Yusuf Bala (Bantex),” a  cewar sanarwar.

Bantex ya kasance Mataimakin Gwamnan Jihar Kaduna a tsakanin shekarar 2015 zuwa 2019, a wa’adin mulkin Gwamna El-Rufai na farko.

A shekarar 2019 ce ya ki neman tazarce tare da Gwamna El-Rufai, domin neman kujerar dan Majalisar Dattawa mai wakiltar shiyyar Kaduna ta Kudu, amma ya sha kasa a hannun Sanata Danjuma La’ah na jam’iyyar PDP.