✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohon Minista ya zama dan takarar Sanata na PDP a Jigawa

Ya taba yi wa jam'iyyar PDP takarar Mataimakin Gwamna a Jihar Jigawa a zaben 2015.

Tsohon Ministan Harkokin Kasashen Waje, Dokta Nuruddeen Muhammad ya yi nasarar lashe zaben zama dan takarar Sanatan a jam’iyyar PDP a Jigawa ta Gabas.

Tsohon Ministan, wanda kuma ya taba kula da Ma’aikatar Watsa Labarai ta Tarayya ya lashe zaben ne babu hammayya a wani zaben cikin gida na musamman da aka yi a ranar Alhamis a garin Hadejia, da ke Karamar Hukumar Hadeja ta Jihar Jigawa.

A yayin da yake yin jawabin amincewa, dan takarar ya gode wa dukkanin wakilan jam’iyyar da suka zabe shi saboda wannan karramawa da suka yi masa.

Tsohon Ministan ya kuma jawo hankalin al’umma ma su zabe da su fito kwanso da kwarkwata wajen kada kuri’a a Babban Zaben 2023 da ke tafe.

Kazalika, ya sha alwashin tunkarar matsalolin da suke addabarsu al’umma a mazabarsa ciki har da ambaliyar ruwa da kwararowar Hamada da yasar kogin Hadeja da kuma yawaitar ciwon koda da dai sauransu.

Muhammad shi ne wanda ya taba yi wa jam’iyyar PDP takarar Mataimakin Gwamna a Jihar Jigawa a zaben 2015.