✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda masu karbar haraji suka ‘hallaka’ wani direba

Wasu da ake zargin masu tara kudaden shiga ne sun yi sanadiyyar mutuwar wani direban babbar mota a Bridgehead, Onitsha, Jihar Anambra. Shaidu sun ce…

Wasu da ake zargin masu tara kudaden shiga ne sun yi sanadiyyar mutuwar wani direban babbar mota a Bridgehead, Onitsha, Jihar Anambra.

Shaidu sun ce masu karbar harajin sun bi matashin direban mai shekara 25 ne a guje, har motar ta kwace masa ya yi karo da wani shinge da aka yi na kankare.

An garzaya da matashin a suma zuwa asibiti inda aka tabbatar da cewa ya mutu, lamarin ya fusatsa wasu matasan yankin suka tare babbar hanyar suka yi ta kone-kone kafin daga baya a lallashe su.

Kakakin ’yan sandan jihar, Haruna Mohammed, ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, John Abang, ya ba da umarnin gudanar da bincike a kai.

Mohammed ya ce: “Ranar Lahadi mun samu rahoton mummunan hatsarin mota a kan babbar hanyar Asaba-Onitsha wanda ya ritsa da babbar mota kirar Marsandi 911 mai lamba, ACA-178-XA, dauke da katakai ta wani mai suna Michael Okorie da ke Oduma a Karamar Hukumar Aninri ta Jihar Enugu.

“Hatsarin ya faru ne lokacin da motar ta kwace wa direban wanda ake zargin masu karbar haraji da ke aiki a Headbridge, Onitsha, sun biyo shi a guje ya daki shingen kankare a da Kasuwar Coca-Cola.

“Sakamakon haka ya sume kuma ’yan sintiri da ke sashin Okpoko suka garzaya da shi asibitin Toronto inda likita ya tabbatar da mutuwarsa”, inji shi.