✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun harbe mutum 10 suna kan hanyar zuwa cin kasuwa

Rahotanni sun ce an kai harin ne garin da ake kan iyakar kasar da Jamhuriyar Nijar.

Akalla mutum 10 ne wasu mahara da ake kyautata zaton ’yan bindiga ne suka harbe ranar Litinin suna kan hanyar zuwa cin kasuwa a kasar Burkina Faso.

Wani jami’in gwamnati a yankin ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na AIB cewa maharan sun kuma yi awon gaba da wasu mutum hudu yayin harin.

An kai harin ne kan mutane da ke cin kasuwa a kauyukan Dambam Markoye da ke dab da iyakar kasar da Jamhuriyar Nijar.

Garuruwan dai na da nisan kimanin kilomita 16 daga kan iyakar kasar da Jamhuriyar Nijar.

Kazalika, AIB ya rawaito cewa tuni sojojin kasar su ma suka mayar da martanin gaggawa a yankin don kaucewa kai wani sabon harin.

Galibi dai mazauna garin na Dambam kan tafi Markoye don cin kasuwa duk ranar Litinin ko dai a kafa, ko a babur mai kafa uku ko kuma a keken shanu don cinikin dabbobi.

Kasar Burkina Faso dai kamar makwabtanta da dama a yankin ma fama da matsalolin tsaro na ayyukan ’yan ta’adda, masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa da kuma ’yan bindiga.