✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan haya sun lakada wa mai gidansu duka

Uwa da ’yarta sun yi wa mai gidan taron dangi suka lakada masa duka har da rauni

Wata mata da ’yarta sun lakada wa mai gidan da suke haya dukan tsiya saboda ya hana su tallata kayansu a gaban gidansa.

A ranar Laraba ne aka gurfanar da matar wadda ’yar tireda ce mai shekara 54, tare da ’yarta mai shekara 29, a gaban wata kotun Majistare da ke Okitipupa, Jihar Ondo bisa zargin duka da kuma jikkata mai gidan duka.

Ana zargin su da aikata laifuka uku da suka hada da tayar da zaune tsaye, kai hari da kuma aikata laifi.

Dan sanda mai gabatar da kara, ASP Zedekiah Orogbemi, ya shaida wa kotun cewa su biyun da wani mutum daya da ya tsere, a ranar 16 ga watan Yuli, da misalin karfe 11 na safe sun hada baki wajen hana zaman lafiya.

Orogbemi ya ce wadanda ake tuhumar sun yi wa mai gidansu, Mista Samson Olakaye dukan tsiya, saboda ya hana su baje kolin kayayyakinsu a kofar gidansa.

Orogbemi ya ce wanda ya shigar da karar ya samu raunuka a lokacin.

Sai dai kuma wadanda ake tuhumar sun musanta aikata zargin.

Alkalin kotun, Chris Ojuola, ya bayar da belinsu a kan kudi Naira 40,000 kowannensu sannan ya dage sauraron karar zuwa ranar 16 ga watan Agusta da muke ciki.