✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Muna bukatar mata da dama a fagen siyasa — Ganduje

Za mu tallafa wa mata da ke hankoron kujerun siyasa a zaben 2023 da ke tafe.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano, ya sha alwashin tallafa wa mata da ke hankoron kujerun siyasa a zaben 2023 da ke tafe.

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN) ya ruwaito Gwamnan yana cewa ana bukatar mata da dama a fagen siyasa.

Ganduje ya yi wannan kira ne a yammacin ranar Litinin yayin wani taron manema labarai a wani bangaren na ci gaba da murnar bikin Ranar Dimokuradiyya.

Ya ce tun ba yanzu, jam’iyyar APC mai mulki a jihar Kano ta rika tallafa wa mata masu burin siyasa wajen cimma muradunsu.

“Duk da cewar jam’iyyar ta bai wa mata kofa bude ta mallakar takardun neman izinin takara a mukaman siyasa daban-daban, amma ba su ribaci wannan dama da aka basu ba.

“Sai dai duk da gazawa da nokewar da suka yi wajen cimma burinsu, gwamnatin ta bai wa galibinsu mukamai na siyasa,” inji shi.

Rahotanni sun bayyana cewa, baya ga bai wa mata mukamai da dama a jihar, gwamnatin Ganduje ta sake sauya fasalin ma’aikatun jihar tare da kara yawan mata a ofisoshin gwamnati da kuma na siyasa.