✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dillalan Shanu da kayan abinci za su janye yajin aiki

Za mu janye yajin aikin safarar kayan abinci da shanu zuwa Kudancin Najeriya.

Shugabannin dunkulalliyar kungiyar dillalan shanu da kayan abinci ta kasa AUFCDN, sun amince za su janye yajin aikin safarar kayan abinci da shanu zuwa Kudancin kasar.

Sun yanke shawarar hakan ne a ranar Laraba yayin wani zaman tattaunawa da suka gudanar tare da Gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi a Abuja.

Abdullahi Tom, daya daga cikin dillalan shanu wanda ya halarci taron, shi ne ya shaida wa Aminiya matakin kungiyar na janye yajin aikin.

Aminiya ta ruwaito cewa, kungiyar AUFCDN wadda wani bangare ne na kungiyar kwadago ta kasa, ta tsunduma yajin aiki ne a ranar Alhamis bayan karewar wa’adin kwanaki bakwai da ta bai wa gwamnatin tarayya ta biya mata bukatunta.

A makon jiya ne kungiyar ta lashin takobin cewa yajin aikin zai ci gaba da dorewa musamman wajen ganin ta dakile isar kayan abinci da dabbobi zuwa Kudancin Najeriya.

A kan hukuncin da kungiyar ta yanke, tana son gwamnati ta bai wa mambobinta kariya tare da biyanta diyyar naira biliyan 475 kan kisan da aka yi wa ’ya’yanta da kuma asarar da ta tafka a yayin zanga-zangar EndSARS da kuma rikicin kasuwar Sasa a Ibadan, babban birnin Jihar Oyo.